Luke 1

Gabatarwa

1Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu, 2kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara. 3Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus, 4don ka san gaskiyar abubuwan da aka koya maka.

An Yi Faɗar Haihuwar Yohanna Mai Baftisma

5A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ʼyar zuriyar Haruna ce. 6Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. 7Sai dai ba su da ʼyaʼya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.

8Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah, 9sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuriʼa, bisa ga alʼadar aikin firist, yǎ shiga haikalin Ubangiji yǎ ƙone turare. 10Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna adduʼa.

11Sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare. 12Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi. 13Amma malaʼikan ya ce masa: “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji adduʼarka. Matarka Elizabet za ta haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa. 16Shi ne zai juye mutanen Israʼila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu. 17Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Eliya, domin yǎ juye zukatan iyaye ga ʼyaʼyansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya-don yǎ kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”

18Sai Zakariya ya tambayi malaʼikan, ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”

19Malaʼikan ya ce, “Ni ne Jibraʼilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi. 20Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”

21Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki mene ne ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. 22Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.

23Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida. 24Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. 25Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”

Annabcin Haihuwar Yesu

26A wata na shida, sai Allah ya aiki malaʼika Jibraʼilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili, 27gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu. 28Malaʼikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.”

29Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka? 30Amma malaʼikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. 31Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. 32Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar mahaifinsa Dawuda, 33zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”

34Maryamu ta tambayi malaʼikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?”

35Malaʼikan ya amsa, ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi
Ko kuwa Saboda haka, yaron da za a haifa za a kira shi mai tsarki,
Ɗan Allah.
36ʼYarʼuwarki Elizabet ma za ta haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. 37Gama ba abin da zai gagari Allah.”

38Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yǎ zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai malaʼikan ya tafi abinsa.

Maryamu Ta Ziyarci Elizabet

39A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, 40inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. 41Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. 42Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! 43Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za ta zo wurina? 44Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. 45Mai albarka ce ita da ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”

Waƙar Maryamu

46Sai Maryamu ta ce:
“Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48gama ya lura
da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,
sunansa labudda Mai Tsarki ne.
50Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,
daga zamani zuwa zamani.
51Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;
ya watsar da waɗanda suke masu girmankai a zurfin tunaninsu.
52Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu
amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa
amma ya sallami mawadata hannu wofi.
54Ya taimaki bawansa Israʼila,
yana tunawa yǎ nuna jinƙai
55ga Ibrahim da zuriyarsa har abada,
kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”

56Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku saʼan nan ta koma gida.

Haihuwar Yohanna Mai Baftisma

57Saʼad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. 58Maƙwabtanta da ʼyanʼuwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.

59A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, 60amma mahaifiyar yaron ta ce, “Aʼa! Za a ce da shi Yohanna.”

61Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”

62Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 64Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. 65Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a koʼina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. 66Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.

Waƙar Zakariya

67Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci, ya ce:

68“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Israʼila,
domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69Ya ta da ƙahon ceto dominmu
a gidan bawansa Dawuda
70(yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
71cewa zai cece mu daga abokan gābanmu
daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu— 
72don yǎ nuna jinƙai ga kakanninmu,
yǎ kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim:
74don yǎ kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu,
yǎ kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,
75cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

76“Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;
gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,
77don ka sanar da mutanensa ceto,
ta wurin gafarar zunubansu,
78saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,
hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,
79don yǎ haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,
da kuma cikin inuwar mutuwa,
don yǎ bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”

80Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Israʼila.

Copyright information for HauSRK